Majalisar dattawan kasar Rwanda ta amince da canza kundun tsarin mulkin kasar jiya Talata matakin da zai baiwa shugaban kasa Paul Kigame damar tsayawa takara karo na uku.
Kafin a canza kundun tsarin sai a kada kuri'un jin ra'ayin 'yan kasar abun da ake gani jama'ar kasar su ma zasu mika kai bori ya hau.
Dokar ta yanzu bata ba Shugaba Paul Kigame damar sake tsaywa zabe ba karo na uku.Kamayayi ya sauka bayan ya gama wannan wa'adin nasa. Wa'dinsa sai kare a shekarar 2017, a lokacin ne kuma wani ya kamata jam'iyyarsa ta tsayar.
Idan za samu aka bari ya sake tsayawa zabe yana iya cigaba da lashe zaben kasar har zuwa shekarar 2034 idan da rai da lafiya.
Kasar Rwanda tana cikin kawayen Amurka na kut da kut a nahiyar Afirka. amma Amurkan tace bai kamata Shugaba Paul Kigame ya ci gaba da jan ragamar mulkin kasar ba bayan da wa'adinsa ya cika.