Majalisar Dokokin Najeriya Za Ta Koma Bakin Aiki Gobe

Majalisar Dokokin Najeriya za ta dawo aiki gobe Talata 28 ga wata Afrilu, bayan hutun mako hudu wanda ya biyo bayan bullar cutar coronavirus.

Shugaban Kwamitin tsare-tsare da walwala na majalisar Abubakar Hassan Fulata ya yi hira ta musamman da wakiliyar muryar Amurka, inda ya ce, idan sun dawo bakin aiki za su yiwa dokar killacewa garambawul, yadda zata baiwa shugaban kasa damar ikon killace al’ummar Najeriya daga duk wata cuta mai yaduwa.

Haka kuma ya ce, zasu duba batun cin zarafi da ake yi wa bakaken fata a kasar China, sannan za su yi gargadi mai karfi wanda idan China bata daub kwakkwaran mataki ba, zai shafi harkokin diflomasiyya da cinikayya tsakanin kasashen.

Ya ce, a cikin batutuwan da zasu gabatar harda kudirin dokar kulawar gaggawa ga ma’aikatan kiwon lafiya da sayo masu kayyakin aiki da zasu kare su daga kamuwa da cutar COVID-19.

Saurari Karin bayani cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

Majalisar Dokokin Najeriya Za Ta Koma Bakin Aiki Gobe