Majalisar Dokokin Najeriya za ta dawo aiki daga hutun ta na shekara da ta tafi, sai dai daga dukan alamu za ta dawo cikin ruguntsumin shugabanci duba da yadda shugabanin ta biyu suka chanja sheka daga jam’iyyar APC mai mulki kuma mafi rinjaye a Majalisar zuwa ta PDP mai adawa.
WASHINGTON D.C. —
Tun ranar 24 ga watan Yuni ne Majalisar ta tafi hutunta na shekara, da aka sa ran zai kare ranar 25 ga watan Satumba da ta gabata. Amma Majalisar ta kara wa’adin hutun da makonni biyu, domin baiwa ‘yan Majalisar damar fafatawa a zabukan fidda gwani na jam’iyyunsu.
Ga dukkan alamu Majalisar za ta dawo cikin rigingimun shugabanci, saboda sauya jam’iyyu da shugabanninta biyu suka yi, wato da Bukola Saraki da Yakubu Dogara.
Sanata Ahmed Babba Kaita, ya ce zasu tursasawa shugabannin idan har basu ajiye mukamansu ba da kansu. Amma mai magana da yawun magoya bayan Yakubu Dogara, ya ce zai yi wuya a tsige shugabannin.
Domin karin bayani saurari rahotan Medina Dauda.
Your browser doesn’t support HTML5