Majalisar Dokokin kasar Rasha ta amince da daukar matakin tsuke bakin aljihu

Masu zanga zanga kin amincewa da tsuke bakin aljihu a kasar Girka

Majalisar kasar Girka ta amince da wani kudurin tsuke bakin aljihu mai muhimmanci da zai hanata gaza biyan bashin dake kanta cikin wannan watan.

Majalisar kasar Girka ta amince da wani kudurin tsuke bakin aljihu mai muhimmanci da zai hanata gaza biyan bashin dake kanta cikin wannan watan. Akasarin membobin majalisar dokokin 300 sun amince da shirin rage Ero biliyan takwas kwatankwashin dala biliyan arba’in na kudin da ake kashewa da kuma karin haraji yau Laraba, da suka hada da mataimakin jam’iyar ‘yan gurguzu Alezandros Athannsiadis wanda a lokutan baya ya kekasa kasa yace ba zai amince da shirin ba. Kungiyar tarayyar Turai da kuma asusun bada lamuni na duniya sun bukaci Girka ta dauki matakin tsuke bakin aljihun kafin a amince da bada bashin Euro 12 daga cikin kudin da aka amince da kasar shekara mai zuwa domin taimaka mata farfadowa daga komadar tattalin arzikin da take fama da shi. Idan ba tare da wannan tallafin ba, kasar Girka zata gaza gudanar da ayyukan kudi a tsakiyar watan Yuli. An kada kuri’ar ne yayinda ake fito mu gama tsakanin yan sanda da masu zanga zanga a kofar majalisa.