Majalisar Dokokin Jihar Kano Ta Dakatar Da Bincikenta Akan Sarkin Kano

Majalisar dokokin jihar Kano ta dakatar da aikin bincike akan mai martaba sarkin Kano Malam Muhammad Sanusi, bisa zarge zarge guda 8 wadanda suka hada da tuhumar kashe kudaden masarautar ba bisa ka’ida ba.

Kimanin makonni biyu da suka gabata ne Majalisar Dokokin ta Kano ta kaddamar da aikin bincinken, wanda nan take da kafa wani kwamiti da zai binciki masarautar.

Tun farko dai wakilin Nasarwa a Majalisar, Ibrahim Ahmad Gama, shine ya gabatar da kudurin da ke neman bincikar sarkin Kano, Mallam Mohammadu Sanusi na biyu, bisa wasu tuhume-tuhume guda takwas. Wanda kuma yayiwa Muryar Amurka bayanin cewa mai martaba yana tsoma kansa cikin harkokin siyasa, wanda hakan ke zubar da kima da mutunci na masarautar Kano.

Yayin da ya rage kwanaki biyu kafin wa’adin da Majalisar ta baiwa kwamitin na makonni biyu ya cika, kwatsam sai gashi jiya Litinin shugaban Majalisar Kabiru Alhassan, ya sanar da dakatar da wancan bincike.

Da yake bayyana dalilan Majalisar na dakatar da wannan bincike, shugaban kwamitin Labaran Abdul, ya ce “mai girma gwamna ya rubuto takarda wacce yake neman alfarmar Majalisar Dokokin jihar Kano, da cewa ta dakatar da wannan bincike. Kuma bisa ga wasu manyan mutane na ‘kasa tun daga kan fadar shugaban ‘kasa, wanda mataimakin shugaban ‘kasa ya nemi wannan alfarma.”

Haka kuma Labaran Abdul, ya ciga da cewa manyan ‘yan kasuwa da ke ‘kasar irin su Aliko Dan Gote da sauran mutane irinsu dattawan Arewa da sarkin Musulmi duk sun nemi alfarmar a dakatar da binciken.

A baya dai hukutmar yaki da rashawa ta jihar Kano ta fara gudanar da binciken zargin yin ba dai dai ba akan mai martaba sarkin Kano Mallam Mohammadu Sanusi na biyu. Amma shigar da Majalisar Dokokin Kano ta yiwa al’amarin ta sanya tilas hukumar ta dakatar da nata binciken, yanzu dai abin jira a gani shine ko hukumar zata sake dawo da nata binciken.

Domin karin bayani saurari cikakken rahotan Mahmud Ibrahim Kwari.

Your browser doesn’t support HTML5

Majalisar Dokokin Jihar Kano Ta Dakatar Da Bincikenta Akan Sarkin Kano - 4'03"