A cewar wanda ya mallaki gidan rediyon Mr. Lawali Aboki sun kammala duk wasu matakan gudanar da aikinsu har ma gwamnan jihar ne Alhaji Umaru Tanko Al-Makura ya kaddamar dashi.
Ranar Juma'a da ta gabata aka mannawa ginin gidan rediyon jan fenti. Washegari ranar Asabar da safe aka rusa gidan rediyon da duka kayan aikin dake ciki.
A cewar Mr. Aboki da misalin karfe takwas ranar Asabar 'yansanda da manyan jami'an gwamnati suka shiga harabar gidan rediyon suka rusashi duk da cewa sun biya harajinsu har na wannan shekarar ta 2017. Suna da takardar mallakar filin da aka gina gidan rediyon da duk wasu takardun da suka kamata suna dasu.
Mr. Aboki yace yana tsammanin gwamnatin jihar ta fusata ne saboda bayyana abubuwan da ma'aikatan kwadago da yanzu suke yajin aiki suke fada. Gwamnati taki a tattauna da ita akan lamuran 'yan kwadagon kuma bata son a tattauna dasu 'yan kwadago.
An yi kiyasin cewa kamfanin rediyon yayi hasarar kumanin Naira miliyan 40 ban da kudin ginin gidan. Wannan na kayan aikin dake cikin ginin ne kawai.
Akan matakin da zasu dauka Mr. Aboki yace zasu hadu a kotu.
Daraktan hulda da mutane na gwamnatin jihar Nasarawa Umar Muhammad Tukur yace gwamnati ta dauki matakin ne kan gine-ginen da ba'a yisu bisa tsari ba.
Ga rahoton Zainab Babaji da karin bayani.
Facebook Forum