A kalla kashi daya cikin hudu na ‘yan majalisar a wannan karon mata ne, abin da ake ganinsa a matsayin wani ci gaba, a kokarin cike gibin dake tsakanin jinsin mata da na maza wajen rabon mukaman siyasa a kasar, inda mata su ka fi yawa.
Da wani kwarya kwaryan buki ne aka kaddamar da ayyukan sabuwar Majalisar Dokokin kasar ta Nijar, mako guda da shudewar wa’adin tsohuwar majalisar, wadda aka kafa bayan zaben shekarar 2016. Majalisar wacce ainahi ke da kujerun wakilci 171, na kunshe ne a wannan karon da wakilai 166 saboda rashin gudanar da zaben ‘yan Nijar mazauna kasashen waje.
Honarabul Kalla Moutari wanda ke daga cikin sababbin ‘yan majalisar dake soma wa’adin wakilicin al’uma na tsawon shekaru biyar, ya ce “Allah sa mu fara lafiya mu kare lafiya, Allah sa wadannan shekaru biyar su ne mafari na kara ci gaban a kasarmu kuma ina fatan saura ‘yan majalisar za su tsaya tsakaninsu da Allah su tabbatar da dokoki na gari.”
Dagewar mata a kan batun mutunta dokar “loi sur le quota” dake hangen ware kaso na musamman domin jinsin mata wajen rabon mukaman siyasa da na nade nade, ta samar da kyakkyawan sakamako, domin a wannan karon mata ne ke kan kashi daya cikin hudu na yawan kujerun wakilcin al’uma a zauren majalisar. A cewar Honarabul Nana Jubi Harouna Maty, hakan na nufin an bude sabon babin siyasa a wannan kasa.
A ci gaba da ayyukan kafa rassan sabuwar majalisar, a yau bangarorin da ke wakilci zasu gudanar da zaben shugabaninsu, a matsayin wani matakin share fagen soma ayyukan da talakkawa ke jiran gani daga wakilansu.
A ranar 27 ga watan Disamba ne ‘yan Nijar suka kada kuri’ar zaben ‘yan Majalisar Dokokin kasa wanda a karshensa jam’iyar PNDS ta zo kan gaba a yawan kujeru yayinda jam’iyar Moden LUMANA ke danne mata gargada sannan sauran jam’iyu suka biyo baya.
Ga wakilin Muryar Amurka a Yamai, Souley Moumouni Barma da cikakken rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5