Majalisar dokokin Jamhuriyar Nijar ta amince da kasafin kudin shekara 2019 da kuri’u 129 daga cikin 171. Akasarin ‘yan majalisar sun yi na’am da wannan kasafi yayin da wakilai 33 su ka nunawa adawa da kasafin kudin.
Ministan Kudi Massaoudou Hassoumi dake halartar wannan zama ya yabawa ‘yan majalisar saboda a cewarsa, wannan babban makami ne ku ka bawa gwamnati don ganin ta gudanar da mahimman aiyukan kasa, idan kuka lura fiye da rabin kasafin zai maida hankali ne wajen aiyukan gina kasa.
A jajibirin zaman majalisar wasu kungiyoyin fafutika da suka shafe kwanaki suna nazarin tsarin kasafin na 2019, sun shawarci wakilan al’umar su yi watsi da wannan kasafi akan wasu dalilai.
Miliyan 2050 na CFA ne gwamnatin ta Nijer ke bukata domin tafiyar da harakokin wannan kasa a badi ta hanyar kasafin da ya tahalakka ga kudaden harajin cikin gida a wani lokacin da akasarin ‘yan kasar ke fama da fatara.
Ga cikakken bayani daga Sule Mumuni Barma
Your browser doesn’t support HTML5