Majalisar Dokokin China Ta Soke Kayyade Wa'adin Shugaban Kasa

Shugaban China Xi Jinping

Biyo bayan amincewar da jam'iyyar kasar China tayi na cewa shugaban kasa ya ci gaba da mulki har iya bakin ransa, yanzu majalisar dokokin kasar ta tabbatar da hakan jiys alashsdi

Majilisar Dokokin kasar China ta jefa kuria jiya Lahadi wanda ya soke adadin shekarun da shugaba zaiyi kan karagar mulki.

Wnnan yana nufin kenan shugaba Xi Jinping zai iya ci gaba da mulki har sai ranar da yaji ya gaji ya sauka ko rai ya yi halinsa.

Ba don wannan sabon dokar ba, ya kamata ace waadin shugaban zai kare ne a shekarar 2023, wannan yasa masu kula da al’amurran yau da kullun na cewa ba mamaki shugaban yaci gaba a mulkin kasar.

Wannan sabon tsarin dokar da aka tabbatar jiya lahadi zai baiwa shugaba Xi cimma manufar sa a siyasance, wanda wannan shine shugaban China na farko da ya samu wannan damar tun bayan shugaban ta na farko Mao Zedong