Majalisar Dokokin Amurka Ta Fara Daukar Matakin Tallafawa Bakin Haure

‘Yan majalisar dokokin Amurka sun amince da wata doka don magance rikicin da ake fuskanta dangane da hanyoyin tallafawa bakin hauren dake kwararowa ta kan iyakar kasar da Mexico.

Shirin dokar na neman a tanadi kudi sama da dala biliyan 4 daga kudaden da aka ware na agajin gaggawa don agazawa bakin hauren da aka tsare, musamman yara.

Kuri’ar da aka kada inda ‘Yan majalisa 84 suka amince da dokar wasu su 8 kuma suka ki, na zuwa ne a daidai lokacin da ake cigaba da sa ido akan yadda gwamnatin Trump ke kula da masu kananan shekaru, a yayinda kuma mutuwar wani mutum dan kasar El Salvador da diyarsa a lokacin da suka yi kokarin tsallaka rafin Rio Grande zuwa Amurka ya janyo suka sosai.

“Babu tantama yanayin da ake ciki a kudancin iyakar kasarmu babban tashin hankali ne ta fuskar taimakon agajin jinkai da tsaro,” a cewar Sanata Richard Shelby na jam’iyyar Republican daga jihar Alabama, ya kuma ce babu dalilin da zai sa a yi jinkiri wajen daukar mataki.