Jirgin Ruwan Da Muka Saka A Kasafin Kudi Ba Na Shugaba Tinubu Ba Ne – Gwamnatin Najeriya

Majalisar Dokoki ((Facebook/Femi Adesina))

Kasafin kudin wanda ya fayyace abubuwan da za a yi da kudaden, na dauke da naira biliyan 5.09 da za a ware domin sayen jirgin ruwan alfarma, lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce a tsakanin 'yan Najeriya.

Fadar Shugaban kasa a Najeriya ta ce kudin jirgin ruwa na shakatawa da aka saka a kasafin kudin cike gibi na rundunar sojin ruwan kasar ne ba na Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba ne.

A ranar Alhamis Majalisar Dokokin Najeriya ta amince da karin kasafin kudi da ya kai naira tiriliyan 2.17.

A kasafin kudin, an ware Naira biliyan biyar na jirgin ruwa, Naira biliyan 2.9 na motocin motsa jiki na fadar shugaban kasa, da kuma Naira biliyan 2.9 don maye gurbin motocin da ke aiki a fadar shugaban kasa.

Wasu da dama na ganin duba da halin da al’umar ksar suke ciki tun bayan janye tallafin man fetur, ba daidai ba ne a ware makudan kudade don sayen wadannan kayayyaki musamman jirgin ruwan.

Sai dai cikin wata sanarwa da ta fitar dauke da sa hannun mai bai wa shugaban kasa shawara a fannin bayanai da tsare-tsare, Bayo Onanuga, Fadar Shugaban kasar ta Najeriya ta ce jirgi ne na musamman da za a saya domin sojin ruwan Najeriya.

“Abin da aka ayyana a matsayin jirgin ruwan fadar shugaban kasa a cikin kasafin kudin, kwale-kwale ne na samar da tsaro na musamman ba don amfanin shugaban kasa ba.

“Ana kiransa da jirgin ruwan Shugaban kasa ne saboda irin manyan na’urorin tsaro da yake tattare da su na musamman.” Onanuga ya ce cikin sanarwar wacce ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Ya kara da cewa, “Shugaba Tinubu, mutum ne da ya fahimci irin matsin tattalin arzikin da jama’a ke fuskanta. Kuma gwamnatinsa na aiki tukuru don ganin ta shawo kansu. Nan ba da jimawa ba, ‘yan Najeriya za su fara girbar sauye-sauyen da ake aiwatarwa wadanda za su inganta rayuwar jama’ar kasar.”

Majalisar kasar dai ta dauki matakin karkatar da kudaden da aka ware a baya zuwa na rancen dalibai, inda ta kara yawan kudaden da aka ware wa a wannan fanni zuwa Naira biliyan 10, wanda ya ribanya kan yadda aka samar da Naira biliyan 5.5 a farkon kasafin kudin.

Majalisar Dokokin Najeriya

Shugaban Kwamitin Kasafin Kudi na Majalisar, Abubakar Bichi Abubakar na jam’iyyar APC ta Kano ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan zartar da kasafin kudin.

A karkashin wannan kasafin kudi da aka yi wa kwaskwarima, kwamitin ya kuma kara kasafin kudin ma’aikatar tsaro daga biliyan 476 zuwa biliyan 546 saboda tabarbarewar tsaro.

Bichi ya kara tabbatar da cewa majalisar ta amince da mafi karancin albashin ma’aikata, inda ya jaddada muhimmancin sa ido a kan majalisa don tabbatar da aiwatar da wadannan gyare-gyaren kasafin kudi.

Da farko dai karin kasafin ya hada da ware naira biliyan 5.09 domin siyan jirgin ruwan shugaban kasa a cikin kasafin kudin rundunar sojojin ruwan Najeriya.

Kasafin kudin rundunar sojin ruwan Najeriya ya bukaci biliyan 62.8 domin gudanar da ayyukansu, inda kudaden da ake kashewa a kai-a kai da manyan kuɗaɗen sun ci biliyan 20.4 da biliyan 42.3, bi da bi.

Sai dai Bichi ya fayyace cewa an fitar da kudaden da aka ware wa jirgin ruwan shugaban kasa daga cikin kasafin kudin gaba daya.

Shugaba Bola Tinubu

Amincewar Majalisar Dokoki ta Kasa na karin Naira Tiriliyan 2.176 na shekarar 2023 da Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu ya mika, ya kara tabbatar da karkatar da kudaden zuwa sassa da ake ganin masu muhimmanci ne sosai.

Babban rabon tallafin ya ƙunshi sassa da hukumomi daban-daban, tare da mai da hankali musamman kan kudaden da aka ware na abubuwan da ka taso, Ma'aikatar Tsaro, Ma'aikatar Ayyuka ta Tarayya, Fadar gwamnati, Ma'aikatar Noma da Abinci ta Tarayya, Ma'aikatar Gidaje, Hukumar tsaro ta farin kaya, Gwamnatin Tarayya. Hukumar Gudanar da ayyuka na Babban Birnin Tarayya, sashen ‘yan sanda, Ofishin mai ba da shawara kan tsaro na kasa, hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta da sauransu.

A karshe, a ranar Alhamis, Majalisar Dokokin Najeriya ta amince da shirin karin kasafin kudin cike gibin bayan sauye sauye da ta yi.

Amincewar majalisar ta zo ne bayan gabatar da rahoton da shugaban kwamitin kasafin kudi Sanata Adeola Olamilekan ya gabatar a yayin zaman majalisar.

-Yusuf Aminu Yusuf