Majalisar Dokoki Ta Ba Babban Akanta Janar  Kwana 60 Ya Dawo Da Naira Biliyan 665.8

Zauren majalisar dattawan Najeriya (Facebook/Nigerian Senate)

Zauren majalisar dattawan Najeriya (Facebook/Nigerian Senate)

Majalisar Dattawa ta umarci Ofishin Akanta Janar na Tarayya Najeriya da ya dawo da kudi Naira biliyan 665.8 da aka karkatar daga asusun bunkasa fannin ma’adanai na kasar.

Bayanan hakan na kunshe ne cikin wani rahoto da kwamitin sauraren bahasi na majalisar ya fitar, inda ya bayyana cewa an karkatar da kudaden ne daga asusun bunkasa fannin albarkatun Kasa da kuma asusun daidaita ayyuka na kasar zuwa ga hukumar zabe ta kasa wato INEC da Ma'aikatar wutar lantarki da kuma rundunar sojin Najeriya da dai sauransu

A cikin binciken da Kwamitin da Sanata Mathew Urhoghide ke jagoranta ya gudanar, ya gano cewa hukumomi da dama sun ci moriyar kudaden da aka karkatar daga Ofishin akanta janar na kasar, wadanda kamata yayi a yi amfani da su wajen gudanar da ayyukan da suka shafi bunkasa fannin ma’adinai a kasar

Haka kuma wasu bayanai sun yi nuni da cewa gwamnatin tarrayar kasar ta yi amfani da wasu daga cikin kudaden wajen biyan hakkokin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da mataimakinsa Namadi Sambo, wanda aka kiyasta ya kai Naira biliyan 1.5 a watan Yuni na shekarar 2015.

An kuma gano cewa hukumar INEC ta karbi kimanin Naira biliyan 20 daga Asusun bunkasa Albarkatun Kasa ban da Naira biliyan 17.9 da aka karba daga kudaden da ka zuba a tallafin shigowa da shikafa daga kasashen waje.

Kazalika kuma an ba da Naira biliyan 30 ga hukumar zabe ta INEC don gudanar da babban zaben shekarar 2015.

Sauran ma’aikatu da aka baiwa kudaden sun hada da ma'aikatar harkokin waje ta tarayya wacce ta sami Naira biliyan 3.6 da ma'aikatar ayyuka da ta sami Naira biliyan biyu sai Hukumar kula da ayyukan sufurin jiragen sama a Najeriya da aka ba Naira biliyan 13, da kuma ma'aikatar matasa da wasanni wacce aka ba Naira miliyan 500.

Majalisar dattawa ta yi matsayar ba wa Ofishin akanta-janar din wa’adin kwanaki 60 da ya tabbatar da an dawo da kudaden zuwa ga lalitar da aka cirosu.

Haka kuma ta yi umarnin cewa a tabbatar da duk wasu kudade da za’a fitar daga asusun, an yi amfani da su ta hanyar da ya kamata kuma sai an nemi amicewar majalisa kafin fitar da duk wani kudi daga asusun.