Majalisar Dinkin Duniya Zata Sabunta Takunkumin da Ta Kakabawa Sudan ta Kudu

Shugaban Sudan ta Kudu Salva KIIR

Bai daya kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da sabunta takunkumin da aka kakabawa Sudan ta Kudu na wani wa'adin shekara daya

A ranar Talata da ta gabata wakilan kwamitin suka yi na'am da kudurin sabunta takunkumin.

Kudurin ya tanadi haramta balaguro da hana kasar anfani da kadaririnta dake kasashen waje.

Abun mamaki minti ishirin kawai wakilan kwamitin suka yi suna yin shawarwarin sabunta takunkumin ba tare da wata jainja ba, suka kuma amince su sabuntata.

A yayinda yake yiwa wakilan kwamitin jawabi jim kadan bayan an kada kuri'ar amincewa, wakilin Amurka na musamman kan harkokin siyasa a Majalisar Dinkin Duniya ko MDD David Pressman yace kudurin ya kamata ya nuna wa shugabannin Sudan ta Kudu cewa basu da zabi illa su yi aiki da yarjejeniyar samun zaman lafiya da suka cimma suka kuma kulla. Ma'an dole su tabbatar da zaman lafiya a kasarsu.