Majalisar Dinkin Duniya: Yau Ce Ranar Nakasassu Ta Musamman

A ranar da majalisar dinkin Duniya ta ware don nazarin hanyoyin kyautata rayuwar mutane masu bukata ta musamman, wani dalibi a ajin farko na Jami’ar Umaru Musa da ke Katsina, ya koka da yadda rashin kayan karatu da rubutu na makafi kan zama tarnaki a karatun su.

Dalibin mai suna Lawal Tasiu Mashi wanda har ila yau shi ne shugaban wata kungiyar jihar Katsina ta jin dadin makafi, ya ce kayan karatun makafi na da tsadar gaske, da sai an samu tallafi daga gwamnati ko masu hannu da shuni kafin mallakar su.

Nakasassu A Najeriya

Mashi ya kara da cewa duk lokacin da malami ya ba da aiki a aji a takardar zango ta darasi, sai sun nemi wani mai gani sun biya shi kudi domin ya karanta masu abin da a ka rubuta.

Makahon ya ce rashin tallafin kan kawo mu su matsala inda wasu ma kan jingine karatun don rashin kudin rejista.

Lawal Mashi ya bukaci gwamnatoci a dukkan matakai, da masu hannu da shuni su rika zagawa makarantu don tallafawa masu bukata ta musamman, domin haka ne zai rage dawainiya da barace-barace a cikin al’umma.

Najeriya yanzu kan samu masu bukata ta musamman hatta a matsayin malamai a jami’o’i.

Ga rahoto cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

Majalisar Dinkin Duniya: Yau Ce Ranar Nakasassu Ta Musamman