Majalisar Dinkin Duniya Ta Zargi Isra’ila Da Kai Hare Hare Kan Jami’an Wanzar Da Zaman Lafiya A Lebanon.

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres

A ranar Juma’a wani jami’in Majalisar Dinkin Duniya ya zargi dakarun tsaron Isra’ila da laifin yawan kaikaitar jami’an wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya dake kan iyakar da aka shata ta wucin gadi tsakanin Isra’ila da Lebanon.

Mai Magana da yawun rundunar jami’an wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya, Andrea Tenenti, ya shaidawa yan jarida a Geneva daga Beirut, cewa, an sha kaikaitar su da hare hare da dama, kuma da gangan

Yace an kai hari kan na’urorin sadarwar su dake dab da inda jami’an wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya suke a fake. Ya kara da cewa, akwai ma lokacin da dakarun rundunar tsaron Isra’ilan suka kutsa kai har wurin da jami’an su suke, suka yi dirshe a wurin har tsawon mintuna 45.

Yace don haka wadannan abubuwa ne dake bayyane a fili, da ba wani nuku nuku a kansu cewa, hare hare ne da ake kaiwa da gangan akan ma’aikatan wanzar da zaman lafiyar na Majalisar Dinkin Duniya.

Isra’ila dai tayi patali da zarge zargen cewa tana kaikaitar jami’an wanzar da zaman lafiyar. Kafar yada labaran Faransa ta AFP ta ruwaito wata sanarwar jami’an sojin Isra’ila na cewa, sam basa kaikaitar wuraren gine ginen jami’an UNIFIL ko Jami‘an su.

Dakarun Isra’ila na gudanar da aiyukan su a kudancin Lebanon a hankoron su na ganin bayan kungiyar mayakan Hezbollah.

To sai dai duk da hakan rundunar dakarun tsaron Isra’ilan ta tabbatar da raunata dakarun wanzar da zaman lafiyar’ UNIFIL ‘biyu, a ranar 11 ga watan Oktoba, lokacin da dakarun suka bude wuta akan abunda wata sanarwar da rundunar ta wallafa a shafin X da aka sani da twitter a baya, ta kira da ‘barazana a nan take’. Rundunar ta kuma bayyana cewa, mayakan Hezbollah a Lebanon, sun gudanar da aiyukan su da gangan, kusa da mazaunin dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya, abinda ya jefa jami’an cikin hadari.

Duk da bukatar primistan Isra’ila Benjamin Netanyahu na cewa, jami’an na Majalisar Dinkin Duniya su janye yana su yana su daga inda aka shata, Tenenti yace, bakin kowa yazo daya kan cewa, kar wanda ya matsa ko ina.