Majalisar Dinkin Duniya MDD ta ce tana marhaban da kubutar da yan mata 82 na makarantar Chibok da yan ta’addar Boko Haram suka yi garkuwa dasu a Najeriya, kuma ta yi kira ga iyalai da jama’a da a taimakawa wadannan yan mata da suke cikin dimuwa.
WASHINGTON D.C. —
MDD ta ce tana kira ga daukacin ‘yan Najeriya da su rike ‘yan matan da hannu biyu, kuma a basu taimako da suke bukata don su ci gaba da rayuwarsu tare da jama’a, inji kakakin sakataren MDD Antonio Guterres a jiya Litinin.
Kakakin Stephane Dujarric yace ana yin watsi da yan mata da aka taba yi musu fyade a cikin al’umma.
Sai dai shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi alkawarin sa ido da kansa a kan kyautata rayuwar ‘yan matan da aka kubutar dasu.
Gidauniyar kula da yawan al’umma ta MDD ta aika da rukunin masana a Najeriya ciki har da masu nasiha da likitoci da zasu taimakawa ‘yan matan su ci gaba da rayuwarsu.