Hukumar dake kula da jin dadin yara ta Majilisar, wato UNICEF tace an jiwa daya daga cikin ma'aikatan ta ciwo shida wani ma'aikacin kwangilar hukumar, wadanda yanzu haka suke wani asibiti suna jinya.
Sai dai hukumar bada bada cikakken nayanin yadda wannan lamari ya faru ba.
Ita dai wannan tawagar ta tafi Borno ne dauke da kayayyakin jin kai daga gari Bama zuwa babban birnin jihar wato Maiduguri, inda nan ne tungan ‘yan boko haram din, UNICEF tace zata kai kayayyakin ne domin ko ana matukar bukatar su a wannan wuri.
Tace wannan harin ba wai ya shafi maaikatar hukumar ta UNICEF bane kawai hatta su kansu wadanda suke sansanin ‘yan gudun hijira ya shafe su domin suna cikin halin oni ‘yasu.
Kungiyar likitocin nan masu bada agaji kyauta da ake kira da turanci Doctors without Borders sunyi gargadin cewa mutane sama da dubu dari biyar a jihar Borno na bukatar taimakon gaggawa.