Majalisar Dinkin Duniya Ta Kebe Kwanaki 16 Don Yin Gangamin Yaki Da Cin Zarafi Da Ya Jibanci Jinsi

SWITZERLAND-UN-POLITICS-DIPLOMACY

Majalisar Dinkin Duniya ta kebe kwanaki goma sha shida don yin gangamin yaki da cin zarafi da ya jibanci jinsi, walau mata ko maza a fadin duniya.

A sakonta ga duniya, Majalisar Dinkin Duniya tace cin zarafi, musamman na mata da 'yan mata ya kasance abin damuwa, wanda yakan shafi mace guda a cikin mata uku a fadin duniya.

Nau'ukan cin zarafin da ake yi wa mata sun hada da fyade, duka, hana su samun ilimi da gamsashshen kiwon lafiya da walwala, yayinda a wasu wurare akan hana mata cin ĝado da tilasta musu yin auren gado wanda ke tauye hakkokinsu na kasancewarsu 'yan Adam.

Wasu mata da yara

A bayaninsa, Malam Abdullahi Sabo jami'in hukumar dake kare hakkin bil'adam ta Human Rights a jahar Filato yace tun alib da tari tara da arba'in da takwas aka kebe wadannan kwanaki don kare hakkin bil'adam.

shima a nasa bayanin, Barista Olivia Dazyam, mai ba gwamnan jahar Filato shawara kan jinsi, yace gangamin na kwanaki goma sha shida ya kunshi fadakar da al'umma su san cewa akwai dokoki da

Kungiyoyin da suka yi gangamin, ciki har da 'yan jarida mata, sun shawarci dukkan wadanda ke fuskantar cin zarafi ta kowace fuska, su sanar da su, don bin diddigi da kwato musu hakkokinsu.

Saurari rahoton:

Your browser doesn’t support HTML5

Majalisar Dinkin Duniya Ta Kebe Kwanaki 16 Don Yin Gangamin Yaki Da Cin Zarafi Da Ya Jibanci Jinsi