Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ranar Lafiyar Kwakwalwa Ta Duniya


Ghana: Ranar Lafiyar Kwakwalwa Ta duniya
Ghana: Ranar Lafiyar Kwakwalwa Ta duniya

Ranar Lafiyar kwakwalwa ta Duniya 2023 da aka yi wa taken: Lafiyar kwakwalwa; hakkin al’ummar duniya ne, dama ce ga duk masu ruwa da tsaki da ke aiki kan lafiyar kwakwalwa da su yi magana game da aikinsu, da abin da ya kamata a yi don tabbatar da ingantacciyar lafiyar kwakwalwa ga mutane a duniya.

A yayin da duniya ta hadu domin bikin ranar lafiyar kwakwalwa ta duniya a ranar 10 ga watan Oktoba, bayanai daga wani shiri na musamman na tantance yanayin lafiyar kwakwalwa a Ghana na Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), na nuni da cewa yanayin lafiyar kwakwalwa a kasar na fuskantar kalubale.

Kimanin mutane miliyan 2.3 ne ke fama da larurar lafiyar kwakwalwa, tare da samun gibin jinyar masu fama larurar da kashi 98%.

A jawabinsa na bukin ranar lafiyar kwakwalwa ta bana, shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), Dokta Tedros Ghebreyesus yace:

"Mutum 1 cikin 8 na rayuwa tare larurar lafiyar kwakwalwa, amma duk da haka a duniya, yawancin mutane ba su samun ingantacciyar kulawar lafiyar kwakwalwa. Muna kira ga dukkan kasashe da su zuba hannun jari a fannin kiwon lafiyar kwakwalwa, musamman a cibiyoyin al'umma, domin babu lafiya ba tare da lafiyar kwakwalwa ba."

Ranar Lafiyar kwakwalwa ta Duniya 2023, da aka yi wa taken: 'Lafiyar kwakwalwa hakkin al’ummar duniya ne', dama ce ga duk masu ruwa da tsaki da ke aiki a kan lafiyar kwakwalwa da su yi magana game da aikinsu, da abin da ya kamata a yi don tabbatar da ingantacciyar lafiyar kwakwalwa ga mutane a duniya.

Dokta Salisu Ango, likitan kwakwalwa a asibitin koyarwa na Korle Bu dake nan Accra, yace kamar yadda mai hankali yake da ‘yancin bil adama, haka kuma mai larurar lafiyar kwakwalwa ke da wannan ‘yancin.

Haka kuma Dokta Nasiba Tahir, Malamar ilmin kwakwalwa ce a jami’ar Islamiya Ghana, a tsokacinta game da bukin tace, ma’aikatan lafiyar kwakwalwa a Ghana sun tashi tsaye wajen ilmantar da jama’a kan muhimmancin lafiyar kwakwalwa: "Domin kai ne ke rike da kwakwalwa, kuma kai da gangan jiki duka abu daya ne. Domin haka, a kiyaye masu larurar kwakwalwa kuma a taimake su, kada a kyamace su."

Kididdigar hukumar lafiya ta duniya na cewa kimanin mutane miliyan 2.3 ne ke fama da larurar lafiyar kwakwalwa a Ghana, tare da samun gibin jinyar masu fama da larurar da kashi 98%. Kasar na fama da karancin magunguna da kwararrun masu kula da lafiyar kwakwalwa, musamman masu tabin hankali, kowane likita kasa da 1 na kula da masu jinya 100,000; haka kuma masana ilimin halayyar dan adam kasa da 1 ke kula da masu jinya 100,000; wanda hakan ya haifar da babban shinge ga samun kulawa.

Wannan ƙarancin ya sa mutane dake fama da larurar suke jan kafa wajen neman taimako a kan lokaci don damuwar lafiyar kwakwalwarsu.

Dokta Salisu Ango ya ce: "Kasar Ghana, ba za mu ce gwamnati ba ta kokari, amma kulawar da ake bukata ga masu tabin hankali, ba a samun yadda ake bukata."

Ya kara da ce wa hakan lamari da ya dauko asali tun da jimawa daga gwamnatocin baya.

Dokta Ango ya kuma ce ciwon kwakwalwa da ya fi zuwa gare su shi ne larurar damuwa ko depression a turance. Kuma kyama daga sauran al’umma da masu fama da larurar ke fuskanta na kara ta’azzara matsalar lafiyar kwakwalwa.

Saurari rahoton Idris Abdallah:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:33 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG