Ofishin kula da 'yancin bil adama na Majalisar Dinkin Duniya ya gargadi jami'an tsaro kan yadda suke cin zarafin bil adama, kamar yadda wakiliyar Muryar Amurka Lisa Schlein ta ruwaito.
Hukumar ta ce jami'anta na bin sawun abin da ke faruwa kuma an samu akalla mutane 6 da aka kashe kana aka jima wasu 68 rauni cikin masu adawa da gwmanatin shugaba Joseph Kabila.
Ana zargin jai'an tsaron a zanga zangar adawa da gwamnati da ake yi a birnin Kinshasa.
Ofishin ya ce, jami'an na amfani da harsashi mai kisa a duk lokacin da suke kai wa masu zanga-zangar hari.
Yanzu haka gwamnatin ta tsare mutane har 121, kuma bayanai sun yi nuni da cewa an yi amfani da hayaki mai sa kwalla a wurare daban-daban ciki ko har da coci da ma wasu sassan kasar.