Majalisar Dattawan Najeriya Tace Dalilin Kin Tantance Ibrahim Magu Yana Nan

Ali Ndume shugaban masu rinjaye a Majalisar Dattawan Najeriya

Duk da furucin Ali Ndume na cewa shugaban kasa na iya sake gabatar da Ibrahim Magu domin a tantanceshi ya zama shugaban EFCC, Majalisar tace dalilan da suka hana tantanceshi na nan babu abun da ya sauya.

Shugaban masu rinjaye na Majalisar Dattawa yace majalisar bata ki amincewa da Ibrahim Magu ba a matsayin zama shugaban hukumar EFCC amma rahoton dake gaban majalisar ya sa suka dauki matakin da suka dauka.

Ali Ndume yace shugaban kasa Muhammad Buhari na iya sake gabatar da sunan Ibrahim Magu wa majalisar domin ta tantanceshi.

To saidai a shafinta na Tweeter Majalisar tace dalilan da suka hana amincewa da Ibrahim Magu na nan kuma shi ne matsayin majalisar bisa rahoton tsaro da suka samu.

Tun lokacin da aka ki amincewa da Ibrahim Magu aka samu muhawara mai zafi tsakanin Ali Ndume da Sanata Dima Melaye. To saidai shi Ndfume ya gana da shugaba Buhari bayan kuma ya fito daga ganawar yace shugaban ne kadai zai iya kawar da sunan Magu daga tantancewa. Haka kuma Magun na iya cigaba da aikinsa a matsayin mukaddashi na wani lokaci.

Baicin Magun Ali Ndume yace sakataren gwamnatin Lawal Babachir yana da daman kare kansa kan batun wuce gona da iri na batun nome ciyawar Kachalla.

A bayanin Ndume ga 'yan jarida yace rahoto akan Babachir ba cikakken rahoto ba ne kuma yana iya bada bayani ba sai an cigaba da kace na ce ba a cikin jarida.

Ga rahoton Medina Dauda da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Majalisar Dattawan Najeriya Tace Dalilin Kin Amincewa da Ibrahim Magu Yana Nan - 3' 22"