Zababben Sabon Shugaban Majalisar dattawan Najeriya Godswill Akpabio ya yi rantsuwar kama aiki, bayan da Magatakardar Majalisar Sani Magaji Tambuwal ya aiyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben da kuri'u 63 inda abokin hamaiyyarsa kuma tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Abdulaziz Yari ya tashi da kuri'u 46.
Sanata Mohammed Ali Ndume shi ne ya gabatar da Godswill Akpabio ga majalisar dattawan, ga abin da ya bayyana wa Muryar Amurka bayan an kammala zaben shugaban.
Ndume ya ce yana hamdala ga Allah ganin cewa an yi zabe lafiya kuma an gama lafiya tare da fatan zai cika wa al'ummar kasa burinsu kamar yadda Allah ya shirya.
Ndume ya ce shi ya fito ya zabi dan kudu domin a ga cewa Jam'iyyar APC mai mulki, jam'iyya ce mai adalci. Ndume ya ce yana ganin an zo gabar da za a yi mulki kamar yadda ya dace.
Shi ma daya daga cikin wadanda aka yi zaben shugabanin da su, Sanata Abdul Ningi daga Jihar Bauchi, ya yi tsokaci ne akan hujjojin da su ka shi ya zabi tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Abdulaziz Yari, a maimakon wanda aka zaba.
Ningi ya ce an fafata yadda dimokradiyya ta gindaya duk da cewa shi ba ya son salon mulkin APC amma ba shi da wani abu da zai yi, saboda haka Allah ya tsara abin shi, amma Ningi ya ce zai yi kokari ya sake renon Jam'iyyar PDP ta wajen yin kudurori da dokokin da za su ja hankalin yan kasa.
A bangaren Majalisar Wakilai kuma, Tajuddeen Abbas daga Zaria, Kaduna shi ne aka zaba da gagarumin rinjaye, inda ya samu kuri'u 353; sannan abokan hamayyarsa, Ahmed Wase da Aminu Jaji, kowannensu ya samu kuri'u 3 ne kacal, wani abu da ya sa dan Majalisa Hassan Shehu Hussein daga mazabar Nasarawa ta JIhar Kano ya ce yan majalisar sun yi zabe ne na cancanta.
Hassan ya ce sabon Kakakin Majalisar Wakilai Tajuddeen Abbas haziki ne, kuma dama kujerar ta masu rinjaye ce a Majalisar. Hassan ya ce abu ne mai wuya a samu dan adawa a irin wannan zubin. Hassan ya ce babu dan Majalisa wanda ya kawo dokoki masu yawa kamar shi sabon Kakakin. Saboda haka an zabe shi ne a bisa kwarewarsa da kuma cancantarsa.
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya ci zabe ne ba tare da hamayya ba, haka shi ma mataimakin Kakakin Majalisar wakilai Benjamin Kalu .
Saurari rahoton :
Your browser doesn’t support HTML5