Majalisar Dattawan Najeriya ta yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya dauki matakin yi wa rundunar ‘yan sandan kasar garambawul domin inganta ayukanta.
Wannan shawara na kunshe ne a cikin rahoton da kwamitin wucin gadi da Majalisar dattawa ta kafa, domin nazari kan kalubalen tsaro a Najeriya tare da samar da mafita.
Rahoton ya ce, fasa rundunar ‘yan sandan kashi-kashi zai kara wa aikin ‘yan sandan kima da karfi wajen taimakawa tsaro a kasar. Daya daga cikin 'yan Majalisar Dattawan Ahmed Babba Kaita ya jadadda cewa "daukan wannan mataki shi ne zai karfafa harkar tsaron kasa".
A cikin shawarwarin har ila yau, akwai batun cewa shugaban kasa ya kafa majalisar tsaro a shiyoyi da za su kunshi mukaddashin Babban Sufeton 'yan sanda, da kuma shugabanin hukumomin tsaro da ke shiyar.
Amma daya daga cikin wakilan hukumar kula da harkokin ‘yan sanda ta kasa Naja'atu Mohammed ta ce, ba ta amince da wannan shawarwari ba, domin zai ba da dama ne ga Gwamnonin jihohi su nuna iko da karfi akan ‘yan sanda a shiyoyin su.
Haka zalika Kwamitin ya nemi a ba Sufeto Janar na 'yan sanda umurnin kaddamar da ‘yan sandan unguwanni tare da hadin gwiwar masu ruwa da tsaki. Kwararre a kimiyar tsaro ta kasa-da-kasa Yahuza Getso ya ce, ba zai haifar da da mai ido ba, saboda zai karfafa son rai da rarraba kan kasar a fannin addini da bangaranci fiye da abin da ke faruwa a yanzu.
Raton ya kuma ba da shawarar rage karfin aikin ‘yan sanda a tsakiya tare da yin kira ga majalisun jihohi da su samar da dokoki da za su halatta rahoton kamar yadda majalisar kasa ta amince da shi.
Saurari Karin bayani cikin sauti daga Medina Dauda.
Your browser doesn’t support HTML5