Majalisar Dattawan Najeriya ta bi sahun takwararta ta Wakilai wajen amincewa da kudirin dokar Naira dubu talatin a matsayin albashi mafi karanci da za a biya ma’aikaci, bayan an kwashe lokaci mai tsawo ana gwagwarmaya da kungiyoyin kwadago.
Sakataran kungiyar kwadago ta ULC, kwamared Nasiru Kabir, ya ce sun ji dadin matsayin da majalisar Dattawan ta dauka, amma dai sai ma’aiakata sun fara karban kudin tukunna za su nuna farin cikinsu.
Wata ma’aikaciya mai suna, Ummi Yahaya, ta ce ta ji dadi sosai da wannan karin na dubu talatin, ta kuma yi fatan Allah ya sa wannan karin ya yi musu amfani saboda lokacin da aka kara albashin ya zama dubu sha takwas sun yi tunanin zai yi auki amma sai sun je kasuwa sai su ga kayayyaki sun yi tsada.
Wani kwararre a fannin tattalin arziki, Yusha’u Aliyu, ya ce karin zai taimaka wa tattalin arzikin kasa ba wai ma’aikata ba kawai.
Shi kuwa Darekta a Ma’aikatar Al’adu da Wasannin Gargajiya ta Najeriya, Olusegun Runsewe, ya ce dole ne talaka ya duba halin da ya ke ciki domin talaka ne ke cutar dan’uwansa, saboda wasu za su yiwa kayan masarufi karin kudi sosai.
Runsewe ya kuma bada shawarar a daidaita farashin kayayyaki saboda talaka ya ci moriyar karin albashin.
Jama’a sun sa ido su ga irin tasirin da karin zai yi.
Saurari cikakken rahoton Madina Dauda:
Your browser doesn’t support HTML5