Majalisar Dattawan Amurka na shirin fara wata shu’umar muhawara kan bakin haure daga ranar Litini. Muhawarar za ta kasance wata iriya, saboda za a fara ta ne ba tare da ainihin takardar kuduri ba.
Shugaban Masu rinjaye na Majalisar Dattawa Mitch McConnell ya ce za a bude muhawarar ce da wata takardar kudurin doka wadda babu batun bakin haure ciki. Daga baya sai ‘yan Majalisar su bukaci a yi gyara ma takardar.
A cewar McConnell gyarar da za a yi za ta tabbatar da adalci a yayin muhawarar.
‘Yan Majalisar za su tattauna kan kan makomar wasu matasan bakin haure da ke zama karkashin wani shirin da ke kare su daga kora mai suna DACA a takaice. Za kuma su tattauna kan batun gina Katanga akan iyakar Amurka da Mexico, da tsarin shigowa Amurka ta hanyar canki-canki, da tsarin shigowa Amurka ta hanyar gayyatar daga wani dangi da dai sauran batutuwa.