Wakilan Majalisar dattijan Amurka a jiya Talata suka bukaci a kare bayanan mutane yadda ya kamata a dandalin sada zumuncin Facebook. Wakilan sun bukaci haka ne a lokacin da wasu kwamitocin Majalisar dattijan Amurka guda biyu suka yiwa shugaban kamfanin Mark Zuckerberg tambayoyi sosai akan yadda ake amfani da bayanan miliyoyin jama’a ba bisa ka’ida ko da izininsu ba.
Shugaban kwamitin shari’a na Majalisar dattijai, Chuck Grassley dan jam’iyar Republican daga mazabar jihar Iowa yace ko tantanma babu ba’a yiwa masu amfani da dandalin adalci ba. Mr Zuckerberg yace kuskurensa ne kuma yana neman a gafarta masa.
Yayi alkawari cewa za’a kare bayanan mutane yadda ya kamata. Haka kuma yayi magana akan alfaharin yadda ake sada zumunci tsakanin jama’a a dandalin na Facebook.