WASHINGTON DC - Zartar da dokar ya biyo bayan nazarin rahoton Kwamitin Manyan Makarantu da na asusun TETFUND mai talafa musu, wanda shugabansa mai wakiltar mazabar Katsina ta Tsakiya, Sanata Muhammad Muntari ya gabatar.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da kudirin ya tsallake karatu 2 a makon daya gabata.
A makon daya gabata ne shugaban kasa bola tinubu, ya aikewa gamayyar majalisun tarayya da wasika yana bukatarsu su soke tsohon kudirin rancen dalibai (damar zurfafa karatu) tare da samar da sabo.
Sabuwar dokar zata inganta yanayin aiwatar da shirin baiwa daliban manyan makarantu rance ta hanyar magance kalubalen dake tattare da tsarin gudanarwar asusun bada rancen karatu na najeriya (NELF) da abubuwan da ake bukata kafin dalibi ya cancanta da dalilin karbar rancen da hanyoyin samun kudaden da rarrabasu da kuma tsarin da za'a bi wacen biyan rancen.
Matakin Shugaba Tinubu na zuwa ne bayan da aka sanarda dakatar da aiwatar da shirin rancen daliban na wucin gadi.
An kirkiri dokar ne da nufin baiwa daliban manyan makarantun Najeriya damar samun rancen me rangwamen kudin ruwa domin su kammala karatunsu cikin sauki.