Bayan da Majalisar Dattawa ta bada wannan umarni na acire karin kudin wuta hukumar kula da kamfanonin samar da wutar Lantarki tayi. Ta kuma ce kwamitin ta dake kula da makamashi da harkokin kwadago ta kira taron sauraron ba’asin jama’a, domin yin nazari akan batun.
Shugaban kwamitin makamashi da harkokin kwadago a Majalisar Dattawa, Sanata Suleman Nazif, yace wadannan kamfanoni masu samar da wutar lantarki a Najeriya, suna nemane su cuci al’umma ne da yin abinda bai dace ba. Sanata Suleman yace shiyasa yayi kuduri wanda zai shigo da gaggawa a Majalisa.
Masu ruwa da tsaki na kallon wannan yunkuri da Majalisar Dattawa tayi, a matsayin wani abune da dukkan yan kasa zasuyi farin ciki da alfahari da shi, a cewar Mohammed Jamo, shugaban kungiyar bada tallafi ga ‘yan kasuwa ta kasa.
A farkon watan nan ne hukumar kula da kamfanonin bada wutar lantarki tayi karin kudin wuta da ya kai kashi 45 cikin 100.
Domin karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5