Majalisar Dattawan Najeriya ta umarci babban hafsan hafsoshin sojojin Najeriya, laftanar janal Tukur Yusufu Buratai, da kuma sufeto Janar na ‘yan sandan kasar Ibrahim Idriss, da su bayyana a gabanta don yin bayani kan yadda Boko Haram ta yi awon gaba da ‘yan matan sakandaren gwamnati ta Dapchi a jihar Yobe.
‘Dan majalisar dattawa Biodun Olujimi, mai wakiltar jihar Ekiti da ya gabatar da wannan kudiri, ya kuma nemi majalisar ta tambayi manyan jami'an tsaron biyu irin kokarin da suke na kubutar da ‘yan matan na Dapchi da ma ragowar ‘yan matan Chibok.
Kafin wannan gayyata ta majalisa, shugaban sojojin kasa na Najeriya, ya bayyana cewa suna yin iya bakin kokarinsu wajen ganin sun nemo ‘yan matan da aka sace.
Janar Buratai, ya ce an yi kuskurene har mayakan Boko Haram suka sami sukunin sace 'yan mata 'yan makarantar, ya kara da cewa hakan ba yana nufin kungiyar 'yan bindigar ta fara farfadowa ba ne. Ya kara da cewa nan bada jimawa ba in Allah ya yarda za a ceto ‘yan matan.
Ya zuwa yanzu dai babu takamaiman ranar da shugabannin tsaron kasar su biyu zasu bayyana ba gaban majalisar.
Wakilin Muryar Amurka a birnin Abuja Hassan Maina, ya ce tun dai lokacin da aka sace yan matan Dapchin, ake ta cece-kuce tsakanin rundunar soji da ta ‘yan Sanda, da kuma gwamnatin jihar Yobe, inda suke ta nunawa juna yatsa.
Domin gano ko wani bangare na tsaron kasar ne yayi sakacin da ya kai ga sace ‘yan matan, yasa masana tsaro irin su Air kwamanda Baba Gamawa, ke ganin wannan gayyata ta majalisar ba zata rasa nasaba da hakan ba.
Tuntuni dai babban hafsan sojojin sama ya tare a sansanin mayakan sama dake shiyyar arewa maso gabas don sa ido da kansa, kan aikin neman ‘yan matan na Dapchi ta hanyar amfani da jiragen sojoji a dazuzukan dake jajohin Borno da Yobe da ma jamhuriyar Nijar, wadda ke makwabtaka da jihohin biyu.
Shi kuma mataimakin shugaban ‘yan sandan Najeriya, DIG Joshak Habila, ya tare a jihar Yobe, domin kara maida hankali aikin nema da kuma ceto‘yan matan.