Majalisar Dattawa Ta Bukaci Shugaban Najeriya Ya Binciki Gwamnatin da Ta Shude

Ginin Majalisun Dokokin Najeriya

Majilisar Dattijan Najeriya ta bukaci shugaba Muhammadu Buhari daya gaggauta binciken tsohuwar gwamnatin da ya gada domin kwato kudin da suka salwanta a lokacin tsohuwar gwamnatin.

Cikin kudaden da majilisar tace ko harda na shirin nan na rage radadin talauci wanda da turanci ake kira Sure –P.

Majilisar tace wajibi ne tsohuwar gwamnatin ta yi bayani yadda ta kashe kudaden da aka ware domin gudanar da wannan shirin dama sauran shirye-shiryen da aka tsara domin rage talauci cikin kasar.

Sai dai wannan na zuwa ne lokacin da majilisar taki amincewa da shirin cika alkawarin da shugaba Muhammadu Buhari yayi na baiwa matasa mara aikin yi alawus-alawus na naira dubu biyar, kwatankwacin dalar Amurka 25 ko wane wata.

Shugaban hukumar ta Sure-p na farko Christppher Kolade ya ajiye aikin hukumar ne a shekarar 2013 sailin da yace shirin ya kauce wa manufar da aka samar dashi, musammam akan abinda ya shafi cin hanci da rashawa tare da yi wa shirin katsalandar da yan siyasa keyi masa.

Sanata Shehu Sani shugaban kwamitin bada rance na ciki da waje yace ga bisa dukkan alamu jami'an tsohuwar gwamnatin ta Najeriya sun yi anfani da manufofin rage radadin talauci domi azurta kansu.