Majalisar Dattawa Ta Bukaci Gwamnatin Tarayya Ta Binciki Bacewar Janar Alkali

Birgediya janar Victor Ezugu da Manjo janar I M Alkali

Majalisar Dattawan Najeriya ta roki gwamnatin tarayya cewa ta kafa kwamitin bincike mai karfi da zai sa a gano Janar Idris Alkali, wanda ya bace tun watan da ya gabata.

Wanan ya biyo bayan wani kudiri ne da dan Majalisar Dattawa daga mazabar Janar din ya gabatar a zauren Majalisar. Sanata Muhammed Hassan, ya bayyanawa Muryar Amurka dalilin da yasa ya kai kudurin gaban Majalisa.

Sanata Hassan ya ce a makon da ya gabata wani hotan bidiyo ya yi ta zagawa yana nuna cewa ba a san inda Janar Idris yake ba, wanda hakan ne yasa ya ziyarci gidan janar din ya gana da iyalansa domin sanin abin da ke faruwa.

Yanzu haka dai rahotanni na cewa mahukunta sun tura da sojoji zuwa jihar Filato domin neman Janar Alkali, wanda ya bace tun ranar 3 ga wata.

A zauren Majalisar Dattawan ‘yan jam’iyyar adawa ta PDP sun nada Sanata Abiodun Christine Olujimi, a matsayin shugabar marasa rinjaye wadda take ‘yar shekaru 61 me wakiltar jihar Ekiti ta Kudu.

Domin karin bayani saurari rahotan Medina Dauda.

Your browser doesn’t support HTML5

Majalisar Dattawa Ta Bukaci Gwamnatin Tarayya Ta Binciki Bacewar Janal Alkali - 2'23"