Majalisar Dattaban Najeriya za ta Binciki Harin Maiduguri

Ginin Majalisar dattawan Najeriya a Abuja

Sanata Bindo Umaru Jibirilla ya ce harin na Maiduguri abun dubawa ne musamman da yake zaman lafiya ya samu a birnin
Majalisar dattawan Najeriya ta bayyana bacin rai tare da yin tir da Allah wadai da harin bom da aka kai birnin Maiduguri wanda yayi sanadiyar asarar rayuka fiye da arba'in. Majalisar ta ce zata binciki lamarin yayin da yan siyasar jihar ke cece-kuce da zargin juna da hannu a harin.

Majalisar tace dole a binciki harin bom din ganin cewa ya faru ne yayin da harkokin tsaro suka inganta a jahar musamman ma a babban birnin jahar Maiduguri.

Dan majalisar dattawan Najeriya Bindo Umaru Jibirilla mataimakin shugaban kwamitin harakokin soji yayi karin bayani a kan binciken a tattaunawar su da wakilin Sashen Hausa Ibrahim Abdulaziz. Dan majalisar dattawan ya ce harin na Maiduguri abun dubawa ne musamman a daidai wannan lokaci da harakokin tsaro suka inganta kuma ya bukaci a ci gaba da yin addu'o'i don samun zaman lafiya a kasar:

Your browser doesn’t support HTML5

Majalisar dattawan za ta binciki harin Maiuduguri - 1:36