Majalisar Datawan Amurka Ta Amince Da Dokar Stopgap

USA-CONGRESS/SHUTDOWN

Dokar da zata dakatar da rufe ofisoshin gwamnati wace zata bada dama a samarwa gwamnati  kudaden da zata kashe na wucin gadi har zuwa watan Maris.

Da sanyin safiyar ranar Asabar ne majalisar dattawan Amurka ta amince da kudurin dokar stopgap spending wato dokar da zata dakatar da rufe ofisoshin gwamnati wace zata bada dama a samarwa gwamnati kudaden da zata kashe na wucin gadi har zuwa watan Maris.

Sai da aka samu goyon bayan duk majalisun dokokin kasar - da majalisar wakilai mai rinjayen ‘yan Republican da majalisar Dattijai mai rinjayen ‘yan Democrats kafin aka amince da dokar, wanda zata taimaka a kaucewa dakatar da ayyukan gwamnati.

A jiya Jumma'a, shugaba Joe Biden ya ce yana goyon bayan wannan dokar sannan zai rattaba hannu akai don tabbatar da dokar.

Idan aka tabbatar da dokar, zata baiwa gwamnati izinin samun kudaden gudanar da ayyukan ta har zuwa watan Maris, sannan zata samar da dala biliyan $100 a matsayin kudaden da za a kashe a fannin tallafin jinkai, da wasu dala biliyan goma ($10,000,000,000), da zata samar wa manoma. Kashe wadannan kudade baza su yi tasiri wajen kara nauyin bashin da ake bin kasar ba.