A halin da ake ciki kuma ana kira ga kaddamar da wani bincike da ka iya kai ga tsige shugaban kasa Donald Trump.
Sai dai Muller mai bincike na musamman da ya yi murabus kwananan nan bayan ya kammala aikinsa, ba zai bada da bahasi a gaban kwamitin shari’a na majalisar wakilai ba, wanda ke fara wani zaman saurer a gobe Litinin mai take “Darasi daga rahoton Muller, shisshigin shugaban kasa da wasu batutuwan aikata laifuka.”
Kwamitin zai saurari bahasi daga tsofaffin lauyoyin Amurka da wasu masana harkokin shari’a, ciki har da John Dean babban mai bada shaida a babban shari’ar Watergate a shekarun 1970 da kuma tsohon lauyan fadar White House a zamanin mulkin shugaban Amurka na waccan lokaci, Richard Nixon.
A ranar Laraba kuma kwamitin tattara bayanan sirri a majalisa zai yi irin wannan zaman saurare mai take “Darasi daga rahoton Muller”. Kwamitin zai mai da hankali ne a kan bayanan leken asiri masu tattare da matsaloli da rahoton Muller ya kunsa. A nan kuma Muller da ma’aikatansa ba zasu bada bahasi ba, amma kwamitin zai saurari tsofaffin manyan jami’an hukumar binciken manyan laifuka ta FBI da suka hada da Robert Anderson da Stephanie Douglas.
‘Yan Democrats sune ke shugabancin kwamitocin biyu, jamai’iyar dake huskantar rarraban kawuna a kan batun Muller.
Yunkurin da kwamitocin majalisar suka yi na samun cikakkun bayanai a kan binciken Muller ya huskanci matsalolin abin da Trump ke kira hurumi da doka ta bashi a matsayinsa na shugaban kasa da kuma hana masu bada shaida su bayyana gaban majalisa ko kuma su gabatar da takardun shaida.