Majalisa Ta Bukaci A Bayyana 'Yan Majalisa Da Aka Ba Kwangila A NDDC

Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya, Femi Gbajabiamila

Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya, Femi Gbajabiamila, ya bai wa Ministan Ma’aikatar Yankin Naija Delta, Sanata Godswill Akpabio, sa’o’i 48 ya bayyana sunayen ‘yan majalisa wadanda aka baiwa kwangiloli a Hukumar Raya Yankin Naija Delta wato NDDC, tare da kuma bayanai dalla-dalla a kan kwangilolin.

Idan ministan ya kasa fitar da sunayen, Kakakin Majalisar ya ce majalisa za ta yi amfani da karfin ikon da doka ta bata don ta tabbatar da cewa ya yi hakan.

Gbajabiamila ya bada sanarwar ne a lokacin zaman da suka yi jiya Talata, kwana daya bayan da ministan ya yi zargin cewa, mafi yawan kwangilolin da hukumar NDDC ta bayar an bai wa ‘yan majalisa ne.

Yayin bayar da bahasi a gaban Kwamitin Kajalisa Wakilai akan NDDC a ranar Litinin, Sanata Akpabio ya yi ikirarin cewa ‘yan majalisa su ne suka fi amfana da kwangilolin NDDC.

A lokacin da aka tambaye shi ta yaya ‘yan Majalisa suka fi amfana, Sanata Akpabio ya ce “Na fada muku cewa muna da bayanan da za su nuna cewa yawancin kwangiloli na NDDC an bai wa membobin majalisa dokoki kasa ne”.

Yanzu an zuba ido aga ko ministan zai bayyana sunayen ‘yan majalisar da ya yi ikirarin an basu kwangilolin kusan kashi 60 ciki 100, kafin wa’adin sa’o’i 48 da majalisar ta bashi.