Majalisar Dattawan Najeriya ta yi watsi da rade-radin da ake yi na cewa akwai wani shiri na tauye hakkokin 'yan jarida a kasar, ta hanyar soke dokar da take ba su damar gudanar da ayyukansu.
Shugaban kwamitin kula da harkokin yada labarai da wayar da kan jama'a, Sanata Suleiman Adokwe, ya bayyana hakan yayin wata hira da ya yi da Sashen Hausa na Muryar Amurka a Abuja.
Sai dai kuma ya ce akwai yunkurin da ake yi na mayar da wasu ayoyi yayin da za a soke wasu a karkashin dokar.
"Yawancin dokoki nan ana duba su a ga inda za a gyara domin su zamanto sun yi daidai da mulkin dimokradiyya." Inji Adokwe.
Wannan yukuri na garanbawul ya haifar da takaddama tsakanin 'yan majalisar da kungiyoyin 'yan jaridu a daidai lokacin da majalisar ta ce za ta sauya dokar wacce aka kwashe shekaru 26 ana amfani da ita.
An kafa dokar ce a zamanin mulkin soji a karkashin gwamnatin tsohon Shugaba Ibrahim Babangida, kuma dokar za ta kara karfin iko ne ga kwamitin Majalisar mai Kula da Harkokin 'yan jarida a kasar, domin a magance matsalar labaran karya da kuma ba da damar hukunta 'yan jaridun idan sun yi ba daidai ba.
Amma 'yan jarida na ganin yin wannan bai taso ba, tun da akwai kotu wacce aikinta ta shi ne bi wa mutum hakkinsa idan an yi masa ba daidai ba.
Suna ganin wannan wani mataki ne kawai na son tauye musu 'yancin gudanar da ayyukansu cikin walwala.
Sai dai a cewar Adokwe, "muhimmin gyaran da ke ciki shi ne, 'yan jarida su da kansu za su zama mambobi na wannan"" majalisa ba wai za ta kasance wacce gwamnati za ta rika amfani da ita ba.
Saurari cikakkiyar tattaunawar Medina Dauda da Sanata Suleiman Adokwe:
Your browser doesn’t support HTML5