A safiyar yau ne majalisar wakilai tayi zaman sirri na tsawon sa'a daya da rabi wato karfe goma sha daya zuwa sha biyu da rabi. bayan sun bude kofa ne shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki ya ce zasu koma zauren majalisar wakilai inda zasuyi wani zaman hadin guiwa na sirri, zaman da suka dauki sa'o'i biyu da 'yan mitina.
Wannan ne karon farko da aka yi irin wannan zaman na hadin guiwar tun da aka fara mulkin dimokradiyya shekaru 19 da suka wuce saidai idan shugaban kasa zai gabatar da kasafin kudi ko kuma zaiyi wani jawabi da ya shafi kasa.
Wannan ke nuni da cewa ba karamar magana aka tattauna ba. Amma ana tunanin baya rasa nasaba da harkokin tsaro ko kuma yadda yan majalisa ke takun saka da gwamnatin shugaba Buhari da kuma rundunar 'yan sanda.