WASHINGTON, D.C —
Masu sharhi sun ce nan ba da dadewa ba China za ta bada umarnin rufe ofishin jakadanci Amurka a China - mai yuwuwa a garuruwan Shenyang da Wuhan, a wani mataki na ramuwa ga hukunci da Amurka ta yanke na rufe ofishin jakadancin China a Houston na jihar Texas zuwa yau Juma’a.
Sannan akwai kiraye kiraye a kafafan yada labarai na China da kuma jin ra’ayi a shafin Twitter na kira ga Beijing ta dauki mataki mai karfi na rufe ofishin jakadancin Amurka a Yankin Hong Kong yayin da shugaban Amurka Donald Trump ya nuna yiwuwar rufe wasu ofisoshin jakadancin China a Amurka.
Masu sharhin guda biyu wadanda suka yi magana da VOA sun ce idan matakin rufewar ya cigaba, dangantakar Amurka da China za ta yi kasa sosai, ta kuma kara muni nan gaba.