Mai Yiwuwa Adadin Mace-mace Ya Tsaya a Dubu 60 - Trump

Shugaban Amurka Donald Trump

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce hasashen da aka yi da farko wanda ya nuna cewa adadin mutanen da za su mutu a kasar sanadiyyar cutar coronavirus ba zai kai 100,000 ko 240,000 da aka yi kiyasi a baya ba.

A ranar Juma’a Trump ya fadawa manema labarai a Fadar White House, yana mai cewa mai yiwuwa adadin ya tsaya a 60,000.

Shugaban na Amurka ya kuma ce ba sai an samu tsayayyen kayan gwaji da duniya za ta amince da shi ba kafin a dawo da gudanar da al'amuran da yau kullum ba.

A karshen watan Maris Trump ya tsawaita matakan da aka shimfida har zuwa ranar 30 ga watan Afrilu domin dakile yaduwar cutar ta coronavirus.

“Ina so a dawo da al’amura ba tare da bata lokaci ba,” in ji Trump yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai.

Akwai dai fargabar idan aka kawo karshen rufe kamfanoni da ma’aikatu da kuma jande umurnin ba da tazara bayan kwana 45, ta yi wu a ga karin bullar cutar a sassan kasar.