Manya manyan kamfanonin sada zumunta na yanar gizo, Facebook da Twitter, za su iya fuskantar tirjiya a kasar Birtaniya, biyo bayan wata bukata da mahukunta sukayi a kasar, na su bayyana irin yunkurin kasar Rasha, na kutse da kasar ta yi a lokacin zaben raba gardama na ko kasar Ingila ta fita daga cikin jerin kasashen turai.
Shugaban bincike na majalisar dokokin kasar ya bayyana hakan da cewar idan har kamfanonin suna so a cigaba da amfani da kafofin nasu a kasar, sai sun bada hadin kai wajen gano gaskiya, da irin yunkurin kasar ta Rasha.
An dai ba kamfanonin wa’adin zuwa ranar 18 ga watan Janairu su fitar da duk wani rahoto da ya shafi zaben da aka gabatar a shekarar da ta gabata. Mr. Damian Collins, shugaban bincike na labaran karya da kasar ta Rasha ta wallafa a lokacin zaben.
Shugaban ya bayyana cewar, suna kokarin ganin irin rawar da kasar Rasha, ta taka wajen sauya ra’ayoyin jama’a bisa wasu bayanai da basu da tushe. Hakan ya sa suke bukatar kamfanonin su mika masu duk wasu bayanan tallace-tallace da labarai da aka wallafa a shafufukan su da suka shafi zaben.