Wannan jinya ta baya-bayan nan na zuwa ne yayin karawar da Chelsea ta yi da Real Madrid a makon da ya gabata a gasar Champions League inda ta sha kaye.
Washington D.C. —
Mai tsaron bayan Chelsea Reece James ya tafi jinyar da ba zai dawo ba har sai wata kakar wasa.
James ya ji ciwo ne a kafarsa.
James, wanda ya sha fama da jinya daban-daban, sau 16 Chelsea ta fara wasa da shi.
Wannan jinya ta baya-bayan nan na zuwa ne yayin karawar da Chelsea ta yi da Real Madrid a makon da ya gabata a gasar Champions League inda ta sha kaye.
Ko da yake, ya buga wasan har karshe, amma gwajin da aka masa bayan wasan ya fito da girman matsalar raunin na shi.
Kazalika, dan wasan kungiyar Mason Mount shi mai yiwuwa ba zai sake buga was aba saboda tiyata da za a yi masa.