Wanan mataki da Mai Shari'a Zainab Bulkachuwa ta dauka ya biyo bayan wani dogon zama da aka yi a kotun zaben ne akan bukatar da Jamiyar PDP ta gabatar akan mai shari'a Zainab da ke zaman Shugaba a Kotun Sauraren Kokekoke a akan zaben shugaban kasa da aka yi tsakanin Shugaba Mohammadu Buhari da abokin hamayyarsa Alhaji Atiku Abubakar.
Jamiyar PDP ta nuna cewa idan Alkali Zainab ta ci gaba da zama shugaba a kotun sauraren kararrakin zaben shugaban kasa to ba za a yi masu adalci ba saboda dangantakar Zainab Bulkachuwa da mijin ta wanda ya ci zaben Sanata a Jamiyar APC a zaben na bana da aka yi, da shugaban kasar. Banda haka kuma aka ce dan ta ma ya tsaya takarar kujerar Gwamna har ila yau a karkashin tutar Jamiyar APC mai mulki.
Darekatan Watsa labaran Jamiyyar PDP Adnin Chinwe Nnorom ta yi bayani cewa ba wai koran mai shari'a Zainab aka yi ba, amma an nemi ta sauka ne daga shugabancin kotun domin tana Uwargida ga dan JamiyNuia mai mulki saboda haka ana fargaban cewa, ba za ta yi hukuncin adalci a shari'ar zaben da ya shafe ta ba.
Amma Tsohon Shugaban Hukumar EFCC Alhaji Nuhu Ribadu ya cealkali Zainab ta nuna cewa ita shugaba ce,domin alkalan kotun mutum biyar sun yi ittifakin cewa babu wata doka da ta hana ta ci gaba da aikin ta,duk da haka a ra'ayin kanta ta ajiye aikin.
Sauka da alkali Zainab Bulkachuwa ta yi daga kujerar kotun sauraren kararrakin zabe bai shafi Mukamin ta na Shugabar Kotun daukaka kara ba,hasalima da ita za a zabi wanda zai gaje kujerar ta a kotun sauraren kararrakin zaben.
Saurari cikakken rahoton Madina Dauda
Your browser doesn’t support HTML5