Ana anfani da kalmomi iri, kamar “Dodo” ko “Babban Bala’in da ba’a ga kamarsa ba a cikin shekaru 100” wajen bayyana masifar dake tattare da wata mahaukaciyar guguwa mai iska mai karfin gaske da aka zana wa suna “Matthew” da yanzu haka take fattatakar wasu sassa na Amurka, musamman gabashin jihar Florida.
WASHINGTON, DC —
Yanzu haka wannan guguwar ta hallaka daruruwan mutane a nahityar carribean, ciki harda mutanen kasar Haiti 283 da ta kashe. Izuwa marecen Alhamishin jiya wannan hadarin ya yi karere ne zuwa yammacin tsibirin Bahamas, ya tasar was ashen arewa-maso-yammaci, abinda ke sa ana zaton da safiyar Jumu’ar nan zai dira kan jihar ta Florida.
Ana kiyasta cewa karfin wannan guguwar ya kai maki 4 saboda karfinta, kuma tafe take da iska mai tafiyar kilomita 210 kowace sa’a daya.
Tuni dai shugaban Amurka Barack Obama ya kaddamarda dokar ta-baci a jihohin Florida din da Carolina ta Arewa saboda wannan bala’in da ya abka musu.