Rahottani daga India na cewa mahaukaciyar guguwar nan ta “Fani” da ake fargaban zuwanta, karshenta ta dira a jihar Odisha ta gabashin kasar a yau Jumma’a, inda take tafe da ruwan sama da kuma iska mai karfin gaske.
An ce mutane sama milyan 100 ke kan hanyar wannan guguwar, kuma akalla mutane milyan daya dake bakin gabar tekun sun saurari jan kunnen da gwamnati ta yi musu, tuni sun tashi sun bar garuruwa da kauyukansu.
A Mozambique kuma, hukumomi sun bada sanarwar barkewar masifar cutar Kolera a arewancin kasar a sanadin rashin ruwan sha mai tsabta bayan wucewar guguwar Kenneth da tayi barna mai yawa a kasar.
Yanzu haka ance mutane fiye da goma ne suka kamu da cutar kolera bayan da guguwar, mai karfin maki 4 ta ratsa kasar, inda tazo da iska mai gudun kilomita 280 cikin sa’a daya.
Haka kuma guguwar ta kashe akalla mutane 41.