Kwamitin shari’ar majalisar wakilan Amurka zai ci gaba da zaman jin bahasi yau Alhamis akan rahoton mai bincike na musamman Robert Muller game da yiwuwar katsalandan Rasha a zaben Amurka, amma in dai ba an sami wani canji ba daga baya, Atoni Janar William Barr ba zai bayyana gaban su ba don bada bahasi.
Ma’aikatar shari’ar Amurka, ta fada a daren jiya Laraba cewa, shirin da shugaban kwamitin, dan majalisa Jarrold Nadler ya yi na sa ‘yan kwamitin su yi wa Barr tambayoyi bai dace ba, ma’aikatar ta kuma ce har yanzu Barr na farin cikin ya gana kai-tsaye da ‘yan kwamitin akan tambayoyin da za su yi masa game da Mueller.
Jiya Laraba Barr ya kwashe sa’o’i da dama yana ba da bahasi a gaban wani kwamiti na ‘yan majalisar dattawan kasar akan matakin da ya yanke na cewa ba a hana ruwa gudu ba a gudanar da binciken, da kuma yadda bai bayyana karshen rahoton Mueller akan katsalandan Rasha a zaben shugaban kasa na shekarar 2016 da kyau ba.
Facebook Forum