Mahamudu Bawumia Ya Amince Da Shan Kaye A Zaben Shugaban Kasar Ghana

Wasu yan kasar Ghana na murnar lashe zaben shugaban kasar

A Ranar Lahadi dantakarar jam’iyar New Patriotic Party mai mulki a Ghana, mataimakin shugaban kasa Mahamudu Bawumia ya amince da shan kaye a zaben shugaban kasar, bayan da ya gaza kawar da damuwar al’umma game da tangal tangal din da tattalin arzikin kasar keyi.

Shan kaye a zaben da aka gudanar a ranar Asabar, ya kawo karshen wa’adi biyu na jam’iyar NPP karkashin shugaba Nana Akufo-Addo da ya gamu da matsalar tattalin arziki mafi muni cikin shekaru, da tsadar kayayyaki da dimbin bashi.

Bawumia ya fada a yayin wani taron manema labarai cewa, al’ummar Ghana sun zabi abinda suke muradi, mutanen Ghana sun zabi canji a irin halin da ake ciki, kuma mun girmama zabin su cikin mutuntawa. Bawumia yace tuni ya kira abokin takarar sa na jam’iyar National Democratic Congress NDC, tsohon shugaban kasa John Mahama ya taya shi murna.

Magoya bayan Mahama sun rika murna da hura usur cikin annashuwa, da tuni suka hallara suna bikin murna a wajen hedikwatar yakin neman zaben jam’iyar dake birnin Accra. Mahama ya tabbatar, a shafin sa na X cewa, ya amshi kiran tayin murna da ga Bawumia dangane da nasarar da ya samu a zaben.

Mataimakin shugaban kasar yace, Mahama ya lashe zaben shugaban kasar ba tare da wata hamayya ba, da kuma jam’iyar sa ta NDC da nan ma ta lashe zaben majalisar dokokin kasar.

Batun tabarbarewar tattalin arzikin Ghana dai ya mamaye zaben, bayan da kasar ta yankin Afrika ta yamma mai arzikin Gwal da cocoa da afka cikin matsalolin tattalin arziki da suka hada da faduwar darajar kudin ta, da sai da ya kai ta ga neman agaji daga cibiyar kudi ta duniya har na kudi dala bilyan 3.

Tun da farko mai Magana da yawun NDC Sammy Gyamfi ya shaidawa manema labarai cewa, nazarin sakamakon zaben da jam’iyar ta yi, ya nuna Mahama ya samu kashi 56.35% da ga cikin 100 na kuri’un da aka kada da ya doke Bawumia da ya sa mu kuri’u 41.3%. Gyamfi yace, hakika a bayyane ta ke cewa, al’ummar kasar Ghana sun zabi canji.