Gwamnatin Jamhuriyar Nijar karkashin jagorancin Mahamadu Isuhu ta ce ta samar da ci gaba na a-zo-a-gani a kasar a wa'adinta na biyu.
A jiya Lahadi shugaba Isuhu ya bayyana a gidan talbijin inda ya zayyana ire-iren ci gaban da kasarsa ta samar yayin da ya cika shekaru biyu a wa’adinsu na biyu.
“Ga likitoci da aka samar a asibitoci daban-daban, musamman ma a Maradi da Yamai da kayayyakin aiki da aka samar a asibitocin, hakan ya sa a irin kididdigar da ake yi, an sa Nijar a cikin kasashen da ke kiyaye lafiyar al’umarta.” Inji Ministan raya al’adu kuma kakakin gwamnatin ta shugaba Isuhu, Asoumana Malam Isa.
Ya kara da cewa an samu ci gaba a fannin ilimi yana mai cewa “gano matsalolin da malamai ke da su” a fannin na ilimi “wannan ma ci gaba ne.”
Sai dai gwamnatin ta shugaba Isuhu ta amince da cewa akwai sauran matsaloli da kasar ke fuskanta, kamar na cin hanci da rashawa.
Sai dai kungiyoyin fararen hula na ganin akwai kurakurai da gwamnatin take tafkawa tun bayan da shugaba Isuhu ya samu wa’adi na biyu.
“Shi yana murna ya shekara biyu, mutane kuma suna bakin ciki ya yi shekara biyu yana muzguna masu.” Inji Jami’in fafutuka Gamatou Muhammadu.
Saurari cikakken rahoton Sule Mumuni Barma kan wannan batu:
Your browser doesn’t support HTML5