Batun karfafa zaman lafiya da hada kan ‘yan kasa sune manyan muradan MPR Jamhuriya a yakin neman sake zaben Muhamman Issoufou na Jamhuruyar Nijar a zabe mai zuwa a kasar. Duk da yake dai MNSD Nasara a can baya sun sha zargin ana amfani da wasu don dagula al’amuraran siyasar.
Wasu masu mara masa baya suna nuna cewa zasu mara masa baya, musamman ma da yake da su aka yi masa yakin neman zaben da ya dare mulkin kasar karon farko.
Wasu kuma da ba a rasa ba suna ganin lokaci yayi da zasu yi sabon zabin don ganin yadda Nijar ke bukatar samun ci gaba da shiga sahun kasashen da ke inganta rayuwar mutanen kasar.
Musamman a bangaren ilimi, lafiya da sauran ababen more rayuwa. Wasu kuma ‘yan kasar Nijar na ganin ana amfani da wasu karnukan farautar siyasa wajen sake dagula lissafin siyasar kasar. Wakilinmu Souley Moumouni Barma ya hada mana rahoton da ke makale a kasan wannan rubutun.
Your browser doesn’t support HTML5