Mahajjatan Jihar Kano Da Kaduna Sun Fuskanci Matsalar Abinci

Mahajjatan jihar Kano da na Kaduna da ma wasu jihohin Arewancin Nijeriya ne suka hade a wuri guda wajen rabon abincin mahajjata, lamarin da ya haifar da cunkuso har ta kai ga an gaza tantance ko 'yan wadanne jihohi ne.

yauyin da wakiliyar Dandalinvoa ta isa inda ake rabon abincin, ta sami maniyyatan na ta hayaniya ba’a ko la'akari da cewar akwai mata wajen, kowanne maniyanci na kokarin kutsawa ciki ne domin ya karbi abinci.

A lokaci kalilan sai abincin ya kare sa'annan aka samu zarafin zantawa da wasu, inda Mohammad Sani Sule, yace bai samu abinci ba, ya dai ci sa’a ya sami raba a wajen wani da ya sani wanda ya samu abincin. Aminu Dan-azumi Gwarzo, cewa yayi wasu ne suke karbar kaso da yawa bayan nasu sai su karbe na wasu su kuma handame shi.

Usman Shu’ibu Yankatsari ya ce abinda ya kawo matsalar shine uniform din mahajjatan jihar Kano da Kaduna iri daya ne wannan da daga cikin babban dalilin da ya haifar da matsalar.

Your browser doesn’t support HTML5

Mahajattan Jihar Kano Da Kaduna Sun Fuskanci Matsalar Abinci