Mahaifiyar Sarkin Kano Da 'Yar Sir. Ahmadu Bello Sun Rasu

Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero Lokacin Da Yake Gaisawa Da Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje a Filin Idi.

Allah ya yi wa Hajiya Maryam Ado Bayero matar tsohon sarkin Kano marigayi Ado Bayero kuma mahaifiyar Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero rasuwa.

Marigayiya Mayram Ado Bayero mahaifiyar ta sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, da aka fi sani da 'Mai Babban Daki', mahaifiya ce kuma ga Sarkin Bichi Alhaji Nasiru Ado Bayero.

Majiyoyi daga masarautar Kano ne suka tabbatar wa manema labarai da labarin rasuwarta, kuma sun ce ta rasu ne da misalin karfe tara na ranar Asabar a kasar Masar.

Ana sa ran yin jana'izarta bayan isowar su da Najeriya daga Masar din a yau ko gobe Lahadi.

Ya zuwa yanzu dai, babu wata sanarwa da ta fito daga Masarautar Kano ko gwamnatin jihar Kano game da labarin rasuwar Hajiya Maryam Ado Bayero.

A wata makamanciyar wannan kuma mun sami labarin rasuwar ‘yar marigayi Firimiyan Arewa, Sardaunan Sokoto Sir. Ahmadu Bello.

Hajiya Aishatu, ‘ya ta biyu ta marigayi Sardauna da suka rayu bayan juyin mulkin 1966, ta rasu ne tana da shekaru 75, a wani asibiti da ke birnin Dubai, bayan gajeruwar jiyya.

Aishatu, 'Yar Marigayi Sir Ahmadu Bello Sardauna

Hamshakin dan kasuwa, kuma Magajin garin Sokoto, wanda da ne ga marigayiyar, ya tabbatar da rasuwar ta Aishatu.

Ta bar ‘ya’ya biyar, namiji daya da mace 4, da suka hada da matar Sarkin Sudan Shehu Malami.

Karin bayani akan: Mayram Ado Bayero, Ahmadu Bello, Sokoto, jihar Kano, Nigeria, da Najeriya.

Haka kuma ta bar kanwarta, wadda ita ce ‘yar autan Sardauna, kuma matar marigayi Umaru Aliyu Shinkafi.

Marigayiya Aishatu ‘ya ce ga matar Sardaunan Sokoto Sir Ahmadu Bello da ta tsira daga kisan dakarun sojin da suka yi juyin mulki a shekarar 1966 da aka fi sani da 'Gwaggon Kano', wadda tarihi ya nuna cewa ba ta Kaduna ko da aka yi juyin mulki.